Daga Ali Rabiu Ali Jigawa
Gwamna Malam Umar Namadi na Jihar Jigawa ya gabatar wa Majalisar Dokokin Jihar da kasafin kuɗin shekara ta 2026, har Naira biliyan 901.8, don gudanar ayyukan raya ƙasa a shekara mai zuwa.
Gwamnan ya bayyana kasafin a matsayin shiri mai ƙarfi, wanda ke nufin ƙarfafa ci gaban da aka riga aka cimma tare da hanzarta cigaba a muhimman sassan tattalin arziƙin jihar.
A lokacin gabatarwar, Gwamna Namadi ya bayyana cewa sabon kasafin ya karu da kashi 19.2% a kan na 2025 wanda ya kai N756.3bn, wanda ke nuna jajircewar gwamnatin sa wajen ci gaba da zuba jari a muhimman ababen more rayuwa, inganta noma, haɓaka wutar lantarki, inganta ilimi da lafiya, da kuma ci gaban walwalar al’umma.
Ya ce kasafin ya ginu ne kan dogon shirin jihar da aka tsara a karkashin gudurin gwamnatin 12 (12 point agenda) da kuma Sabon Tsarin Ci Gaban Jihar da aka amince da shi kwanan nan.
Read also: Jigawa state celebrates 34 years of existence
Gwamnan ya yi bayani kan yadda ake sa ran samun kuɗaɗen kasafin, inda ake sa ran tattara N901.8bn daga waɗannan majiyoyin: N96.2bn daga rabon tarayya (Statutory Allocation), N102bn daga VAT, N223bn daga wasu kuɗaɗen tarayya, N88.9bn kudaden cikin gida (IGR), N42bn daga kudaden LEA da PHC, sannan N349.5bn daga ragowar kudi, lamuni da tallafi.
Ya ce an yi nazari sosai kan waɗannan adadi don tabbatar da cewa kasafin na da tushe mai ƙarfi da tabbataccen tsarin samun kuɗi.
Gwamna Namadi ya bayyana cewa tsarin kashe kuɗin kasafin ya nuna fifikon gwamnati na zuba jari a dogon lokaci fiye da yadda ake kashe kuɗi kan yau da kullum, inda aka ware N693.4bn — wanda ya kai kashi 76.9% na gabaɗayan kasafin domin manyan ayyukan raya ƙasa. Sauran kuɗin sun haɗa da N120bn na albashi, N75.6bn na kayan aiki da sauran bukatu, N7bn don tanadi da kwanciyar hankali, da N5.7bn don biyan bashin jama’a.
A bangaren rabon manyan ma’aikatun gwamnati, gwamnan ya bayyana cewa bangaren tattalin arziƙi wanda ya ƙunshi hanyoyi, noma, wuta, kasuwanci, jari-hujja da ƙarfafa matasa ya samu fiye da N396bn, ciki har da N186.3bn domin ci gaban hanyoyi da sufuri, N74.9bn don noma da kiwo, N50.7bn ga wutar lantarki da makamashi, N17.5bn ga kasuwanci da jari-hujja, N17.4bn ga zuba jari na musamman, da N12.6bn don ƙarfafa matasa da samar da ayyukan yi.
Ya ce wadannan jarin za su taimaka wajen inganta hanyoyi, ƙara yawan amfanin gona, tabbatar da wutar lantarki mai dorewa, faɗaɗa kasuwanci da samar da ayyukan yi ga matasa.
Bangaren walwalar jama’a shima ya samu gagarumin kaso fiye da N236bn, inda ilimi da lafiya suka samu kaso mafi girma: N48.2bn ga ilimin asali, N52.3bn ga post-basic, N38.6bn ga manyan makarantu (tertiary), N27.2bn ga Ma’aikatar Lafiya, N20.1bn ga hukumar kula da kiwon lafiya a matakin farko (PHCDA), da N13.9bn ga harkokin mata da walwalar jama’a. Sannan bangaren Labarai, Matasa, Al’adu da Wasanni ya samu N2.8bn.
Gwamna Namadi ya ce jimillar rabon da bangarorin ilimi da lafiya suka samu wato sama da N310bn ya nuna mahimmancin ci gaban dan Adam a matsayin ginshiƙin bunkasar jihar. Ya kuma jaddada cewa gwamnati ta ware kuɗaɗe don inganta ruwa, kare muhalli da raya birane.
Wadannan sun haɗa da N25.4bn don samar da ruwa da tsaftace muhalli, N35.4bn don kare muhalli da tsaron yanayi, N7.9bn don filaye, gidaje da ci gaban birane, da N2.3bn ga kananan hukumomi da ci gaban al’umma.
Wadannan jarin za su taimaka wajen samar da ruwan sha, dakile ambaliyar ruwa da kwararar ƙasa, rage barazanar sauyin yanayi, da inganta tsare-tsaren birane da yankuna.
A lokaci guda, Gwamna Namadi ya kuma gabatar da hadadden kasafin kuɗin kananan hukumomi 27 na jihar, wanda ya kai N288,848,892,051, inda aka ware: N68,884,969,458 don albashi, N74,265,000,320 don kayan aiki, N8,100,000,000 don kudin tanadi, da N137,598,273,000 don manyan ayyukan ci gaba.







