Daga Ali Rabiu Ali, Dutse
A cikin wani sabon yunƙuri na ƙara wayar da kan jama’a da tabbatar da cikakken halartar al’umma a kamfen ɗin rigakafin Polio na watan Nuwamba 2025, Hukumar Lafiya matakin Farko ta Jihar Jigawa (JSPHCDA), tare da haɗin gwiwar Hukumar Kula da Kiwon Lafiya matakin Farko ta Ƙasa (NPHCDA) da abokan aikin kawar da cutar shan-inna (GPEI), ta shirya babban taron tattaunawa da kafofin yada labarai domin wayar da kai da kuma motsa al’umma.
Wannan taro, wanda UNICEF ta shirya a babban birnin jihar Dutse, ya tattaro ’yan jarida, masu tasiri, a ranar 25 ga Nuwamba 2025, da babban manufar karfafa gwiwar iyaye, masu kula da yara, al’umma da masu ruwa da tsaki domin goyon bayan zagayen rigakafin polio na gaba a jihar.
A jawabin sa, shugaban ofishin UNICEF na Kano, Mr. Rahama Rihood Fara, ya jaddada cewa kafofin yada labarai muhimmin abokin aiki ne wajen tsara fahimtar jama’a da tabbatar da bin tsarin rigakafi a al’umma.
Karin labari: Gwamna Namadi ya gabatar da kasafin kuɗi na sama da Naira biliyan 901
Ya yi gargadin cewa dole ne ’yan jarida su ƙara yada sahihan bayanai kan kamfen ɗin rigakafin polio na Nuwamba 2025, musamman a yankunan karkara inda bayanan ƙarya da jin kai game da allurar rigakafi ke ci gaba da bayyana.
An bayyana a taron cewa akwai bukatar gaggawa ta yada bayanai game da muhimmancin rigakafin polio, motsa al’umma da shugabannin gargajiya don shiga cikin kamfen ɗin, tare da bibiyar yadda ake gudanar da rigakafin kai tsaye a kananan hukumomi 27 na jihar.
Nura Ado, mataimakin jami’in ilimantarwa akan harkar lafiya na JSPHCDA, ya tabbatar da cewa hukumar na da niyyar ci gaba da kare nasarorin da aka samu wajen kawar da polio, tare da tabbatar da cewa babu wani yaro a Jigawa da ya rasa rigakafin da zai kare rayuwarsa.
Haka kuma taron ya haɗa da tattaunawa da shugabannin matasa da masu tasiri a kafafen sada zumunta, wadanda suka yi alkawarin yada saƙonnin wayar da kai a dandalin intanet da cikin al’umma.
Yayin da babban kamfen na Nuwamba 2025 ke gabatowa, masu ruwa da tsaki na fatan cewa karfafa haɗin gwiwa da kafofin yada labarai zai ƙara yawan yara da za su samu rigakafi kuma ya taimaka wajen kiyaye matakin Jigawa a matsayin jiha marar cutar shan inna (polio free state).
Jami’in lura da aiwatarwa da tantance bayanai na JSPHCDA, Zakaria Saleh Shehu, ya bayyana cewa adadin yaran da ake niyya a rigakafa ya kai 1,516,244. Ya kuma yaba wa kafofin yada labarai kan gudunmawar da suke bayarwa wajen wayar da kan jama’a game da rigakafi da sauran batutuwan lafiya.







