Skylink Multimedia.
Hedikwatar tsaron Najeriya ta yi karin haske game da kiran da babban hafsan hafsoshin kasar, Janar Christopher Musa, ya yi, cewa jama’a su fara tunanin koyon dabarun kare kansu da aka amince da su a duk fadin duniya.
Ta ce jama’a sun yi wannan kira wata fahimta ta daban, to amma abin da babban jami’in tsaron ke nufin shi ne ba wai mutane su dauki makami su kare kansu ba, a’a yana nufin su koyi abubuwa kamar kokowa da judo da dambe da ninkaya da gudu dama tukin mota da dai sauransu.
Birgediya Janar Tukur Gusau, shi ne daraktan yada labarai na rundunar tsaron Najeriya, ya shaida wa BBC cewa shi babban hafsan tsaron na nufin cewa a matsayinka na adam bai kamata ka zauna haka kawai ba tare da ka koyi wata dabara da za a kare kanka ba.
Ya ce,” A misali irin mutanen nan da ketare mutane suna kwace musu waya da yawansu wasunsu basa dauke da makami karfi kawai suke nuna wa jama’a, to irin wannan yanayi ne shi babban hafsan tsaron ke ganin ya kamata mutane su koyi dabarun kansu kamar kokawa da gudu, inda duk wanda ya nuna maka karfi kai ma sai ka ware gwanjinka.”
“Maganar a dauki makami ma dokoki na Najeriya ma basu yadda wanda ba shi da hurumin daukar makami su dauka ba, idan kuwa har suka dauki makami to akwai dokar da zata yi aiki a kansu.”In ji Janar Tukur Gusau.
BBC Hausa.






