Home Hausa Jigawa Ta Kammala Samar da Yellow Card Ga Mahajjatan 2026

Jigawa Ta Kammala Samar da Yellow Card Ga Mahajjatan 2026

8
0

Daga Ali Rabiu Ali, Dutse

Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta sanar da kammala samar da katin rigakafi na yellow card ga dukkanin maniyyatan aikin Hajjin shekarar 2026, lamarin da ke nuna wani babban ci gaba a shirye-shiryen jihar na tafiya zuwa ƙasar Saudiyya.

Babban Daraktan Hukumar, Alhaji Ahmad Umar Labbo, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Habibu Yusuf Babura, ya sanya wa hannu, inda ya bayyana nasarar a matsayin wani muhimmin mataki. 

Ya ce yellow card wanda ke zama takardar shaidar rigakafi ta ƙasa da ƙasa, wajibi ne ga duk wanda zai shiga ƙasar mai tsarki.

A cewarsa, hukumar ta fara tsara katunan bisa rukuni-rukuni domin tabbatar da tafiya cikin tsari da sauƙi kafin lokacin tashi.

Labbo ya ƙara da cewa Jihar Jigawa na daga cikin jihohin da ke kan gaba a Nijeriya wajen yin shirye-shiryen Hajjin 2026 cikin lokaci da inganci.

Ya kuma bayyana cewa hukumar na ƙara ƙaimi wajen wayar da kan maniyyata da horas da su a dukkanin ƙananan hukumomi 27 na jihar domin shirya su yadda ya kamata don wannan tafiya ta ibada.

Babban Daraktan ya yaba wa ma’aikatan hukumar bisa jajircewa da haɗin kai da suka bayar, wanda ya taimaka wajen kammala aikin cikin lokaci.

Haka kuma ya gode wa Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, bisa ci gaba da goyon baya da kulawa da harkokin hukumar, yana mai tabbatar da cewa ana ɗaukar dukkan matakan da suka dace domin tabbatar da gudanar da aikin Hajji cikin nasara ba tare da wata matsala ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here